Hausa Waec Answers 2024
(4)
(a) Suna Gama-gari: Shi ne sunan da idan aka ambata shi yake nuni zuwa ga abubuwa da yawa masu jinsi ko nau’i ɗaya. Wato suna ne na tarayya. Dukkan abin da ke da irin wannan jinsi ko nau’i, an yi tarayya da shi a cikin wannan sunan. Misali, mutum, yaro.
(b) Tattarau: Suna ne da ya dunƙule abu fiye da ɗaya a cikinsa. Wato suna ne da ya tattaro abubuwa masu yawa a cikinsa. Misali, garke, ƙungiya.
(c) Wakilin Suna Ɓoyayye: Shi ne wakilin sunan da baya fito da wanda ake magana a kansa fili. Wato idan aka ambata shi, kowa ma yana iya shiga ciki. Misali, wance, su wane.